Isa ga babban shafi
Fashin Teku

An soma yunkurin kafa kawancen magance fashi a mashigar ruwan Guinea

Manyan kamfanonin sufurin jiragen ruwa da masu fito na duniya sun bukaci kafa wani kawancen da zai yi maganin aikata fashin teku dake karuwa a gabar ruwan Guinea inda ake garkuwa da matuka jirage.

Nigerian special forces have been training to combat piracy
Nigerian special forces have been training to combat piracy PIUS UTOMI EKPEI AFP
Talla

Gabar ruwan Guinea da ake sufuri tsakanin Senegal zuwa Angola na fama da matsalar Yan fashin teku musamman Yan Najeriya wadanda ke kai hari kan jiragen ruwa da manyan makamai suna garkuwa da matuka domin karbar diyya.

wakilan wadannan kamfanoni da matuka da yan kasuwa kusan 100 suka sanya hannu akan takardar bukatar kafa kawancen domin tinkarar matsalar, kuma sun fito ne daga kasashen Turai da China da Japan da India da kuma Turkiya.

Akasarin kasashen Turai kan tura jiragen yakin su yankin jifa-jifa domin samar da tsaro ga jiragen ruwan dake wucewa, sai dai ana samun Karin hare haren musamman daga bangaren tekun Najeriya zuwa yankunan dake kusa da shi.

Ko a watan Maris da ya gabata sanda kasar Denmark ta bayyana shirin tura jirgin yaki yankin, bayan kama matukan jirgin ruwan ta 15 wadanda aka sake a watan Afrilu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.