Isa ga babban shafi
Togo

Fashin teku na janyo hasarar makudan kudade a Afrika- Gnassingbe

Shugaban Togo Faure Gnassingbe, ya ce matsalar fashi a kan teku na haddasa wa kasashen gabar ruwa na yammaci da tsakiyar Afirka hasarar dala bilyan 7 a kowace shekara, inda ya bukaci a gudanar da taro domin tattauna wannan matsala a cikin watan Nuwamba mai zuwa.

Shugaban Togo Faure Gnassingbé
Shugaban Togo Faure Gnassingbé AFP PHOTO / ISSOUF SANOGO
Talla

Shafin gwamnatin Togo na Intanet ya fadi cewa za a gudanar da taron ne a ranakun 4 zuwa 7 a Lome babban birnin kasar.

Gnassingbe wanda ke ganawa da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a birnin Abuja, ya ce matsalar satar mai, da fatauci miyagun kwayoyi na daga cikin batutuwan da taron zai tabo.

A cewar shugaban na Togo yaki da ‘yan Fashi teku matsala ce da kasa guda ba za ta iya magani ba dole sai an hada kai.

Shugaban na Togo ya jinjinawa shugaban Najeriya da kuma dakarun kasar dangane da irin galabar da suke samu akan mayakan Boko Haram.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.