Isa ga babban shafi
Afrika

An samu karuwar fashin Teku a yammacin Afrika cikin 2020- IBM

Hukumar da ke sanya idanu kan tsaron Teku ta IMB ta sanar da samun karuwar fashin Teku da hare-hare kan jiragen ruwa cikin shekarar 2020 da akalla kashi 20 idan aka kwatanta da wanda suka faru a 2019.

Kafin yanzu dai mashigin ruwan Aden gefen Somalia shi ne yankin Teku mafi hadari a Afrika.
Kafin yanzu dai mashigin ruwan Aden gefen Somalia shi ne yankin Teku mafi hadari a Afrika. REUTERS
Talla

Cikin rahoton shekara-shekara da IBM kan fitar dangane da tsaron tekun, ta ce an fuskanci fashin Teku sau 195 cikin shekarar 2020 sabanin 162 da aka samu a 2019.

IMB wadda ta bukaci karin hadin kai wajen bayar da cikakken tsaro ga Tekunan Duniya, rahotan na ta ya ce matukan jiragen ruwa akalla 135 aka yi garkuwa da su cikin 2020 kuma 130 daga cikinsu an sace su ne a mashigin Tekun Guinea wanda ke nuna irin barazanar da ke sake dabaibaye harkokin sufurin jiragen ruwa a yammacin Afrika.

Mashigin Tekun na Guinea wanda ya hadar da yanki mai yawa daga kudancin Angola kana wani bangare na arewacin Senegal ana kallonsa a matsayin Teku mafi hadari da karancin tsaro a Duniya.

Daraktan hukumar ta IMB Michael Howlett ya ce masu fashin Tekun sun sauya salo daga sata ko kuma karkatar da jiragen ruwa, maimakon hakan sukan garkuwa da matuka jirgin ne tare da neman fansa.

Mr Howlett ya ci gaba da cewa dole ne har sai kassahen yammacin Afrika sun mike tsaye wajen magance matsalar ne za su iya karfafa tattalin arzikinsu musamman Najeriya da Angola mafiya fitar da Fetur kasashen Duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.