Isa ga babban shafi
Mali-Ta'addanci

Sweden ta aike da dakaru na musamman zuwa Mali

Rundunar sojin Faransa tace Sweden ta aike da dakarunta na musamman zuwa Mali domin kara karfin sojojin kawancen dake fafutukar murkushe kungiyoyin ‘yan ta’adda.

wasu sojojin Faransa yayin tabbatar da tsaro a birnin Gao, dake kasar Mali.  9/3/2013.
wasu sojojin Faransa yayin tabbatar da tsaro a birnin Gao, dake kasar Mali. 9/3/2013. REUTERS/Emmanuel Braun
Talla

Yayin sanar da matakin a ranar Juma’a, kakakin rundunar sojin Faransa Fredric Barbry, yace dakarun na Sweden 150 za su kasance a Mali har zuwa karshen watan Fabarairu.

Yankin da yafi fuskantar hare-haren ta’addanci a Mali dai shi ne wanda yayi iyaka tsakanin kasar da Burkina Faso da kuma Nijar, inda kungiyoyi masu ikirarin jihadi ke da karfi.

A halin yanzu dakarun Faransa dubu 5 da 100 ke girke a Mali don yakar ‘yan ta’adda da hare-harensu ya bazu daga arewacin kasar, zuwa sassan Burkina Faso, Nijar da kuma Chadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.