Isa ga babban shafi
Faransa-Mali

Wani jirgin sama ya kashe mahalarta taron aure 20 a Mali

A yayin da Faransa ke bayyana kashe gomman mayakan jihadi a wani hari jiragen sama da ta kai a makon da ya gabata a yankin tsakkiyar kasar Mali, shaidun gani da ido na bayyana cewa, fararen hula 20 mahalarta daurin aure sun rasa rayukansu a  wani harin jirgi mai saukar angulu da ba a tantance ba.

Sojojin Faransa na Barkhane dake yankin Sahel
Sojojin Faransa na Barkhane dake yankin Sahel Reuters/Benoit Tessier
Talla

A ranar Lahadin da ta gabata kafofin sada zumunta sun yi ta yada jita jitar lamarin da ya faru a kauyen Bounti, inda mazauna kauyen suka sanar da AFP cewa wani jirgi maisaukar agulu ne da ba a tantance ko nawaye ba ya kai harin.

A dai bangaren kuma rundunar sojin Faransa ta sanar da AFP cewa jiragen saman yakinta sun fatataki gomman mayakan jihadi a wani guri dake tsakkiyar kasar Mali bayan da suka kwashe tsawon kwanaki suna bibiyar gungun mayakan sau da kafa.

Sai dai kakakin sojin na Faransa ya bayyana furucin dake cewa an kashe masu halartar daurin aure da cewa basu san da wannan zance ba.

Su dai mazauna kauyen na Bounti sun bayyana cewa jirgin mai saukar angulu ya buda wuta  kan mahalarta daurin auren a tsakiyar rana, abida ya haifar da firgitsi sosai tsakanin mahalarta daurin auren.

kungiyar Fulani ta, Tabital Pulakuu, a kasar Mali, tace jirgin mai saukar agulu ya yi kasa kasa ne kafin bude wuta inda nan take ya hallaka masu halartar daurin auren 20 wasu kuma da dama suka jikkata.

kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya ambato wata majiyar sojin Faransa na cewa sojojin na kasar na da labarin harin na ranar Lahadin da ta gabata.

Kauyen Bounti dai na cikin yankin Mopti ne, mai tazarar kilo mita 600 da Bamako babban birnin kasar ta Mali.

Yankin da ke fama da hare haren mayakan dake ikararin jihadi da ya barke a arewacin kasar ta Mali tun  a shekarar  2012 da ya watsu kasashe Burkina Faso da jamhuriyar Nijar dake makwabtaka da kasar ta Mali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.