Isa ga babban shafi
Mali - Faransa

An gudanar da zanga-zangar adawa da sojojin Faransa a Mali

Jami’an tsaron Mali sun tarwatsa gungun mutane dake zanga-zangar adawa da jibge masu sojojin Faransa a kasar. 

Masu zanga-zanga a Mali
Masu zanga-zanga a Mali AP Photo/Baba Ahmed
Talla

A daidai lokacin da Jami'an tsaron ke tarwatsa masu zanga-zangan a birnin Bamako sai kuma ga wasu ayarin na masu zanga-zangar bisa Babura daga sassan Bamakon za su inda ake boren.

Dama dai Hukumomin yankin sun haramta dukkan taron nuna kyamar sojan na Faransa inda suka danganta da annobar cutar Coronavirus.

Kasar Mali dai na fama da matsalolin masu ikirarin jihadi da karfin tsiya a arewacin kasar tun shekara ta 2012 kafin ma lamarin ya fantsama zuwa su Burkina Faso da Niger.

Kasar Faransa wadda ta yiwa Mali mulkin mallaka, ta shiga don kare kasar a shekara ta 2013 da hana su kaiga birnin Bamako.

Yanzu haka tana da soja 5,100 a yankin na Sahel, amman kuma wasu ‘yan kasar na kushe dakarun Faransan da zargin basa tabuka komai, wajen hana kai hare-haren.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.