Dakarun Barkhane sun hallaka 'yan ta'adda 20 a Burkina Faso
Gwamnatin Faransa tace dakarun ta tare da abokan aikin su, sun yi nasarar kashe mahara masu ikirarin jihadi 20 a arewacin Burkina Faso a makon jiya.
Wallafawa ranar:
kakakin sojin kasar Kanar Frederic Barby yace sun samu bayanan asiri ne lokacin da Yan bindigar su kusan 30 ke tafiya akan babura a Boulikessi dake kusa da iyakar Burkina da Mali da Nijar, abında ya sa aka kai musu hari.
Jami’in yace a wannan rana kuma jirgin yakin dake sarrafa kan sa ya kai hari kan motar maharan dake tafiya akan hanyar N’Daki dake cikin Mali.
Kanar Barby yace dakarun rundunar Barkhane tare da masu taimaka musu na cigaba da kai munanan hare hare a yan kwanakin nan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu