Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Congo

Al'ummar Congo na alhinin cika shekaru 20 da kashe Laurent Kabila

Dubban al’ummar Jamhuriyar Congo sun yi taron alhinin tunawa da tsohon shugaban kasar Laurent-Desire Kabila da aka yiwa kisan gilla shekaru 20 da suka gabata.

Tsohon shugaban Jamhuriyar Congo Laurent-Desire Kabila
Tsohon shugaban Jamhuriyar Congo Laurent-Desire Kabila ODD ANDERSEN/AFP/Getty
Talla

Laurent Kabila shi ne mahaifin tsohon shugaba Joseph Kabila da ya mikawa shugaban Jamhuriyar Congo mai ci Felix Tshisekedi.

Dubban jama’a ne suka yi tattaki zuwa gidan tsohon shugaba Joseph Kabila dake garin Lubumbashi a yankin Katanga, don taya shi alhinin tunawa da mahaifin nasa.

A shekarar 1997 Laurent Desire Kabila ya dare mulkin Jamhuriyar Congo bayan kifar da gwamnatin shugaba Mobutu Sese Seko. Ranar 16 ga Janairun 2001 ne kuma wani dogarin Kabila ya harbe shi har lahira a ofishinsa dake birnin Kinshasa.

A watan Janairun 2003 kotun ta yanke hukuncin kisa kan mutane 39 da aka samu da hannu a kisan tsohon shugaban na Jamhuriyar Congo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.