Isa ga babban shafi

'Yan tawaye sun kashe 'yan kabilar jinsin wadanni 46 a Congo

Hukumomi a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo sun ce jinsin gajerun mutanen nan da aka fi sani da Pygmies 46 ne ‘yan tawayen kungiyar ADF suka kashe a lardin Ituri dake gabashin kasar.

Taswirar Afrika mai nuna Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo.
Taswirar Afrika mai nuna Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo. AFP
Talla

Shugaban wata kungiya mai zaman kanta a yankin, Gili Gotabo ya ce ‘yan tawayen ADF sun kai samame kauyen Abembi, inda suka kashe wadanni 46, suka kuma raunata 2.

Ministan cikin gidan lardin Adjio Gigi, ya tabbatar da aukuwar lamarin, yana mai dora alhakin ta’asar a kan kungiyar ADF, wadanda ake zargi da kisan daruruwan mutane a shekarar da ta gabata.

Harin ya auku ne a wata masarauta da ake kira Walese Vonkutu, da ke iyakar Ituri da arewacin Kivu, a cewar wasu majiyoyi.

Kungiyar da aaka kafa a cikin shekarun 1990 kungiyar ‘yan tawayen ADF ta yi kaurin suna wajen kisan al’umma.

Ana zarginta da kisan daruruwan fararen hula a arewacin Kivu da kudancin Ituri, a wani harin ramuwa kan dirar mikiyar da sojojin kasar suka yi musu a shekarar 2019.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.