Isa ga babban shafi
Burundi

Corona ta kashe tsohon shugaban Burundi

Tsohon shugaban Burundi Pierre Buyoya ya mutu a birnin Paris na Faransa sakamakon kamuwa da cutar Covid-19 yana da shekaru 71.

Tsohon shugaban Burundi Pierre Buyoya
Tsohon shugaban Burundi Pierre Buyoya AP Photo/Keystone, Salvatore Di Nolfi
Talla

Majiyoyin makusantansa sun shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP cewa, Buyoya ya mutu ne a cikin daren da ya gabata.

Tun a ranar Larabar makon jiya aka kwantar da shi a asibiti a birnin Bamako, kafin komawa da shi Paris, inda aka sanya masa na’urar da ke taimaka masa yin numfashi.

A yammacin jiya aka yi balaguro da shi zuwa Paris. Sai dai ya yi ban-kwana da duniya a daidai lokacin da motar daukar marasa lafiya ta kai shi asibiti don fara karbar magani.

A cikin watan Nuwamban da ya gabata ne, Buyoya ya yi murabus daga kuejrar manzan Kungiyar Tarayyar Afrika a Mali bayan kotu ta yi masa daurin rai da rai a Burundi bisa samun sa da hannu a kisan magajinsa a shekarar 1993.

Buyoya ya fara darewa kan kujerar shugabncin Burundi ne ta hanyar juyin mulkin 1987.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.