Sissoco Embalo ya sha rantsuwar kama aiki
Shugaban Guinea Bissau mai jiran gado Umaro Sissoco Embalo yayi rantsuwar kama aiki a jiya alhamis a dai dai lokacin da takaddama tayi zafi tsakaninsa da jagoran ‘yan adawa na jam’iyyar PAIGC Domingos Simoes Pereira, wanda tuni ya garzaya kotun kolin kasar domin kalaubalantar nasarar Umaru Sissoco.
Wallafawa ranar:
A karshen watan Disambar shekarar 2019 bara kenan a zaben shugabancin kasar zagaye na biyu da ya gudana, Umaru Sissoco ya lashe zaben da kashi 53.5, yayinda Periera ya lashe kashi 46 na kuri’un da aka kada, kamar yadda hukumar zaben kasar ta sanar.
Rantsuwar kama aikin Sissico da ya karbi ragama daga shugaba mai barin gado Jose Mario Vaz ya haifar da rudani a tsakanin al’ummar Guniea Bissau ganin cewar kotun kolin kasar ta bada umarnin sake kidayar kuri’un da aka kada.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu