Tsoffin Firaministoci na fafatawa a zaben Guinea-Bissau
Al’ummar Guinea Bissau na kada kuri’a a zaben shugabancin kasar zagaye na 2, cike da fatan kawo karshen rikicin siyasar da kasar ke fuskanta.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Mutane dubu 700 ake sa ran za su kada kuri’a a zaben na yau, wanda za a fafata tsakanin tsaffin Fira Ministocin kasar biyu, Domingos Simoes Pereira na jam’iyyar PAIGC mai mulki da kuma jagoran ‘yan adawa Umaru Sissoco Embalo.
A zagayen farko na zaben da ya gudana a karshen watan Nuwamban da ya gabata, Pereira ya lashe kashi 40 na kuri’un da aka kada, yayinda Embalo ya zo na biyu da kashi, 27 da rabi.
Tun a zagayen farkon ne dai, shugaban kasar ta Guniea Bissau mai ci, Jose Mario Vaz ya fice daga cikin takarar, bayan gaza samun adadin kuri’un da yake bukata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu