Shugaba Jose Mario Vaz ya nada sabon Firaminista a Guinea Bissau
Shugaba Jose Mario Vaz ya nada sabon Firaminista mai suna Umaro El Mokhtar Sissoco Embalo mai shekaru 44 a daren jiya juma'a. Nadin da ke zuwa bayan canji da aka samu na Gwamnati tun bayan sauke Baciro Dja daga wannan matsayi.
Wallafawa ranar:
Sabon Firaministan na daya daga cikin mashawartan Shugaban kasar Jose Mario Vaz,wanda nauyi ya rataya kan sa na sake ceto tattalin arzikin kasar dama kawo karsen rikicin siyasa da ya mamaye jam'iyya mai mulki.
Masu lura da siyasar kasar Guinea Bissau sun bayyana sabon Firaministan kasar a matsayin mutumen dake da kwazo da fahimtar Diflomasiyar kasashe da dama.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu