Isa ga babban shafi
Lafiya

Ebola ta sake yaduwa a Jamhuriyar Congo

Rahotanni daga Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo sun ce, an sake samun wani mutum da ya kamu da cutar Ebola a Goma, birni na biyu mafi girma a kasar, yayinda adadin wadanda cutar ta kashe yanzu haka ya kai 1,790.

An killace mutumin da ya kamu da cutar Ebola a baya-bayan a Jamhuriyar Congo/
An killace mutumin da ya kamu da cutar Ebola a baya-bayan a Jamhuriyar Congo/ REUTERS/Baz Ratner
Talla

Dr. Aruna Abedi, shugaban kwamitin kai dauki ga masu kamuwa da cutar a arewacin Kivu ya tabbatar da samun labarin, wanda aka danganta shi da wani mutum da ya ziyarci Goma daga Ituri ranar 13 ga watan nan.

Farfesa Jean-Jacques Muyembe, jami’in Ma’aikatar Lafiyar Kasar ya ce, tuni aka gano mutumin, kana kuma aka killace shi domin ci gaba da kula da shi.

Hukumomin lafiya na duniya sun bukaci kasashen duniya da su gaggauta bayar da agaji don kawo karshen cutar mai matukar hadari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.