Isa ga babban shafi
Najeriya-Fulani

Gwamnatin Najeriya na shirin fara ginin rugagen zamani ga Fulani

A Najeriya wasu rahotanni na nuni da cewa, gwamnatin kasar ta fara wasu shirye-shiryen samar da rugage na zamani ga Fulani makiyaya a kasar a wani yunkuri na kawo karshen rikicin da ake fuskanta tsakaninsu da Manoma, wanda gwamnatin ke ganin na da nasaba da hare-haren ‘yan bindiga baya ga ayyukan garkuwa da mutane.

Masu makiyaya a Najeriya
Masu makiyaya a Najeriya guardian.ng
Talla

Wata jaridar Najeriyar ta ruwaito cewa, yanzu haka gwamnatin ta ware maka-makan filaye a jihohin kasar 11 don gudanar da aikin samar da rugagen ga Fulani, ciki kuwa har da jihohin Taraba Admawa Pulato da kuma Kaduna.

Sauran jihohin a cewar Jaridar sun hada da Sokoto, Nasarawa, Kogi, Katsina, Kebbi, Zamfara da kuma jihar Niger.

Jaridar ta ruwaito ma'aikatar aikin gona a Njeriyar na cewa, sai da gwamnatin kasar ta tattauna da gwamnatocin jihohi suka kuma amince tare da bayar da filayen gudanar da aikin wanda ke da nufin bunkasa harkokin kiwo a kasar.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.