Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya za ta gina wuraren kiwo na zamani 94 a jihohi 10

Taron majalisar zartaswa ta Najeriya da mataimakin shugaban kasar Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranta, tare da ministoci, gwamnoni, da masu ruwa da tsaki, ya amince da ware kimanin naira biliyan 179, a karkashin wani shiri da zai shafe shekaru 10, domin kawo karshen rikicin manoma da makiyaya a kasar.

Najeriya na hasarar naira kimanin naira triliyan 5 a kowace shekara sakamakon rikicin manoma da makiyaya da kuma rashin kebantattun wuraren kiwo na zamani.
Najeriya na hasarar naira kimanin naira triliyan 5 a kowace shekara sakamakon rikicin manoma da makiyaya da kuma rashin kebantattun wuraren kiwo na zamani. Paulo Santos/Reuters/Corbis
Talla

A karkashin shirin, gwamnatin Najeriya za ta gina kebantattun wuraren kiwo har guda 94 a jihohi 10 da suke fama da matsalar rikicin manoma da makiyaya.

Jihohin sun hada da Taraba, Nasarawa, Filato, Oyo, Zamfara, Adamawa, Benue, Ebonyi, Edo, da kuma Kaduna.

Kashin farko na shirin gina kebantattun wuraren kiwon, zai soma ne a jihohin Benue da Nasarawa ko wane lokaci daga yanzu.

Yayin da suke yi wa manema labarai karin bayan taron a garin Abuja, gwamnan jihar Benue Samuel Ortom, Ministan ayyukan noma da raya karkara na Najeriya, Audu Ogbe, da kuma jagoran shirin gina wuraren kiwon Dakta Andrew Kwasari, sun ce gwamnati, za ta fara fitar da kimanin naira biliyan 70, wadanda za fara amfani da su, daga yanzu zuwa karshen wa’adin farko na shugaba Muhammadu Buhari.

Ministan noma Audu Ogbeh wanda ya ce lokaci ya yi da za a sauya tsarin da makiyaya ke kai na kiwon dabbobinsu, ya ce babu wanda zai kai makiyayan amfana da sabon shirin a nan gaba.

Shugaban shirin gina wuraren kiwon, Dakta Andrew Kwasari ya ce bayaga hasarar rayuka, Najeriya na tafka hasarar akalla dala biliyan 14, kwatankwacin naira triliyan 5 a kowace shekara sakamakon rikicin manoma da makiyaya, la’akari da cewa rikicin na haddasa hasarar kimanin lita miliyan 700 na madara.

Dakta Kwasari ya kara da cewa, a halin yanzu ana iya samun litar madara miliyan 400 ne kawai, a dalilin illar da rikicin manoman da makiyaya ya haifar da kuma rashin samar da wuraren kiwo na zamani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.