Isa ga babban shafi
Sudan

'Yan Sudan za su nada Firaministan da suke so

Sabuwar gwamnatin mulkin sojin kasar Sudan ta bukaci bangarorin siyasa da kuma masu tarzoma da su zabi mutum kamili da za a nada a matsayin Firaministan kasar.

Wasu daga cikin masu zanga-zanga a Sudan
Wasu daga cikin masu zanga-zanga a Sudan 路透社
Talla

Laftana janar Yasser Al-Ata, daya daga cikin mambobi a majalisar koli ta mulkin sojin, shi ne ya bayyana hakan a lokacin wata ganawa da aka yi tsakanin sojojin da kuma ‘yan siyasa a ranar Lahadi.

Yanzu haka sabon shugaban majalisar koli ta mulkin sojin na ci gaba da daukar matakai da suka hada da tube shugaban Hukumar Leken Asirin kasar da kuma tube jakadan kasar da ke Amurka.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da jama’ar kasar ke ci gaba da zanga-zanga don ganin cewa, sojojin sun mika mulki ga fararen hula bayan hambarar da gwamnatin shugaba Omar al-Bashir.

Kazalika masu zanga-zangar sun bukaci a gaggauta gurfanar da al-Bahsir wanda ya kwashe shekru 30 bisa karagar mulkin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.