Isa ga babban shafi
Najeriya

Hukumomin Najeriya sun musanta labarin kama Walter Onnoghen

Gwamantin Najeriya ta musanta rade radin cewar tana shirin kama babban mai shari’ar kasar Walter Onnoghen wanda ake tuhuma da kin bayyana kadarorin da ya mallaka da kuma boye wasu jerin asusun ajiyar sa dauke da makudan kudaden kasashen waje.

Muhammadu Buhari Shugaban Najeriya da babban mai shari’ar kasar Walter Onnoghen
Muhammadu Buhari Shugaban Najeriya da babban mai shari’ar kasar Walter Onnoghen lailasnews
Talla

Wata sanarwar da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai Femi Adeshina ya gabatar, tace babu gaskiya kan wannan labari da aka ce wata kungiyar jam’iyyun siyasa na yadawa.

Adeshina yace fadar shugaban kasa nada labarin tuhumar da kotun ladabtar da ma’aikata ke yiwa Onoghen da kuma wasu kararrakin da aka shigar a kotu kan shari’ar, saboda haka ba za tayi katsalandan a ciki ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.