Isa ga babban shafi
ICC-Gbagbo

Akwai yiwuwar kotun ICC ta wanke Laurent Gbagbo

Sashen daukaka kara na kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC ya fara wani zaman sauraran shari’ar tsohon shugaban kasar Ivory Coast Laurent Gbagbo yau Litinin bayan wasu hujjoji da ke nuna cewa babu gaskiya a zarge-zargen da ake yi kan tsohon shugaban.

Laurent Gbagbo mai shekaru 73 shi ne shugaban kasa na farko da aka gurfanar gaban kotun ta ICC a shekarar 2011.
Laurent Gbagbo mai shekaru 73 shi ne shugaban kasa na farko da aka gurfanar gaban kotun ta ICC a shekarar 2011. REUTERS/Luc Gnago/Files
Talla

Tsohon shugaba Laurent Gbagbo wanda kotun ke tuhuma da laifukan take hakkin bil’adama lokacin tashe-tashen hankulan da suka faru a kasar bayan zaben 2010, kuma ya ke tsare a hannun kotun tsawon shekaru 7, acewar lauyan da ke kare shi Emmanuel Altit akwai yiwuwar zaman kotun na yau ya iya wanke shi daga zarfe-zargen da ake masa bisa ga hujjojin da su ke da shi a hannu.

Emmanuel Altit ya shaidawa zaman kotun cewa tun farko bangaren adawa ne suka tayar da rikicin da ya kai ga kisan jama’a wanda kuma jami’an tsaron kasar suka dauki matakan dakatar da rikicin.

Lauyan ya kara da cewa ko kadan jami’an tsaron kasar basu farmaki bangaren adawar ba, face kokarin kare kansu da suka rika game da hare-haren da ‘yan adawar.

Sai dai kotun na ganin tun farko Gbagbo ne ya ruruta wutar rikicin kasar bayan kin amincewa da shan kaye a zaben kasar da ya nuna Alassan Ouattara ne ya lashe, matakin da ya haddasa rikici tsakanin bangarorin adawa tare da sabbaba kisan fiye da mutane dubu 3.

Laurent Gbagbo mai shekaru 73 shi ne shugaban kasa na farko da aka gurfanar gaban kotun ta ICC a shekarar 2011 bayan nasarar kame shi karkashin jagorancin wasu dakaru masu samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya da kasar Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.