Dramani Mahama zai sake tsayawa takarar shugabancin Ghana
Tsohon shugaban Ghana John Dramani Mahama, ya bayyana aniyarsa ta sake tsayawa takara a zaben shugabancin kasar da za’a yi a cikin shekaru biyu masu zuwa.
Wallafawa ranar:
Mahama, wanda ya mulki kasar tsawon shekaru 4 daga 2012 zuwa 2016, ya gaza samun nasara a zaben shugabancin kasar da ya gudana a shekarar ta 2016, wanda abokin hamayyarsa wato shugaba mai ci Nana Akufo-Addo ya lashe.
Tsohon shugaban na Ghana ya bayyana aniyar tasa ce a sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya ce tuni ya mika takardar neman izinin jam’iyyar adawa ta NDC ta tsayar da shi takara.
A tsakanin watan Oktoba zuwa Nuwamba jam’iyyar NDC za ta gudanar da zaben fidda gwani tsakanin masu neman ta basu takarar shugabancin Ghana tsakanin tsohon shugaban kasar, John Dramani Mahama, da kuma sauran masu neman takarar guda 4.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu