Isa ga babban shafi
Ethiopia-Eritrea

Habasha ta kawo karshen rikicin kan iyaka da Eritria

Gwamnatin Ethiopia karkashin jagorancin sabon Firaminista Abiy Ahmed ta amince da kawo karshen rikicin kan iyakar da kasar ke yi da makociyarta Eritrea wanda ke da nufin bunkasa bangaren tattalin arzikinta.

Sabon Firaministan Ethiopia Abiy Ahmed.
Sabon Firaministan Ethiopia Abiy Ahmed. REUTERS/Tiksa Negeri
Talla

Eritrea wadda ke a matsayin wani yanki na Ethiopia kafin rikicin neman ballewarta a shekarar 1998 zuwa 2000, wanda ta kai ga Ethiopia kin amincewa da hukuncin majalisar dinkin duniya na ayyana yankin a matsayin kasa mai cin gashin kanta, yanzu haka na rike da manyan hanyoyin bunkasa tattalin arzikin yankin ciki har da gabar teku.

Tun bayan da ya karbi iko da kasar a cikin watan Aprilu bayan tsawon shekarun da aka shafe ana adawa da gwamnatin kasar, Firaminista Ahmed ya daura damarar samar da sauye sauye tare da dai daita al’amura wanda ke da nufin samar da sauyi ga tattalin arzikin kasar ciki har da bunkasa harkokin sufurin jiragen saman kasar.

Cikin wata sanarwar bazata da ke zuwa bayan jam’iyya mai mulki ta EPRDF ta sanar da dokar takaita zirga-zirga da aka saba duk shekara a ilahirin kasar, ta ce zata ci gaba da amfani da dokar samar da hukumar kula da iyakoki ta 2002.

A cewar jam’iyyar ta na fatan Eritrea za ta amshi kudurin na su cikin gaggawa tare da dai daita rikicin da ke tsakaninsu.

Tun bayan kammala rikicin kan iyakar kasashen biyu na Ethiopia da Eritrea kowannensu ya dauki hanya daban don bunkasa tattalin arzikinsa, inda Ethiopia ke a matsayin mafi bunkasar tattalin arziki cikin sauri a bara, ko da dai Asusun bada lamuni na duniya IMF y ace akwai yiwuwar tattalin arzikin ya sakko zuwa kasha 8.5 sabanin kasha 10.9 da ya kai a bara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.