Isa ga babban shafi

Shugaban hukumar kare hakkin dan adam na ziyara a kasar Habasha

Babban jami’in hukumar kare hakkin dan adam na majalisar dinkin duniya, Zeid Ra’ad al-Hussien ya sauka a kasar Habasha, inda zai ziyarci yankin Oromia da ya yi fama da zanga-zangar kin jinin gwamnati tsawon shekaru uku.

Shugaban hukumar kare hakkin dan adam ta Majalisar Dinkin Duniya Zeid Ra'ad al-Hussein.
Shugaban hukumar kare hakkin dan adam ta Majalisar Dinkin Duniya Zeid Ra'ad al-Hussein. REUTERS/Pierre Albouy
Talla

A shekarar da ta gabata ma dai Ra’ad al-Hussien ya yi kokarin ziyartar yankin amma gwamnatin kasar a waccan lokacin ta ki bashi dama.

Ziyarar ta shugaban hukumar kare hakkin dan adam ta majalisar dinkin duniya ta zo ne bayan rantsar da sabon Fira Ministan kasar ta Habasha, Abiy Ahmed, makwanni uku da suka gabata.

Yayin ziyarar Zaid Ra’ad al-Hussien ya gana da shugabannin yanin Oromia inda suka tattauna hanyoyin samar da zaman lafiya da kuma cimma bukatunsu ga gwamnati cikin ruwan sanyi.

Zuwa yanzu gwamnatin Habasha ta saki daruruwan fursunonin siyasa da ta kama yayin zanga-zangar kin jinin gwamnati a yankin na Oromia, a wani bangare na maido da kwanciyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.