Isa ga babban shafi
Dimokuradiyar Congo

Taron samarwa yan gudun hijirar Congo kudade a Swiziland

A taron Geneva na samarwa yan gudun hijira kudade, taron ya gudana dai ne inda manyan kasashen Duniya suka dau alkawalin samarwa kasar da kudaden da za su baiwa kungiyoyin agaji damar samarwa yan gudun hijira da abinci mai gina jiki.

Yan gudun Hijira a Jamhuriyar Dimokuradiyar Congo
Yan gudun Hijira a Jamhuriyar Dimokuradiyar Congo JOHN WESSELS / AFP
Talla

Rashin bada hadin kai daga hukumomin gwamnatin Jamhuriyar Dimokuradiyar Congo ya kawo cikas ga kokarin kasashe 54 da suka gudanar da wannan taro a Geneva.

Akala yan gudun hijira milyan 7 da dugo 7 ne suke cikin mauyacin hali musaman suke fuskantar karancin abinci, yayinda sama da yara milyan biyu ke fama da cutar tamowa.

Kasashe 54 ne suka halarci taron tarawa kasar kudade na Geneva tareda yi alkawura na taimakawa da kudade, akala ana bukatar bilyan daya da milyan dari 7 da za su taimakawa domin magance wannan matsala a Jamhuriyar Dimokuradiyar Congo.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.