Isa ga babban shafi
DRC

An kashe mutane a zanga-zangar adawa da Kabila na Congo

Jami’an tsaron Jamhuriyar Demokradiyar Congo sun harbe mutane shida har lahira tare da cilla hayaki mai sa kwalla don tarwatsa masu zanga-zangar adawa da shugaba Joseph Kabila.

Masu zanga-zangar adawa da shugaba Kabila a birnin Kinshasa
Masu zanga-zangar adawa da shugaba Kabila a birnin Kinshasa JOHN WESSELS / AFP
Talla

Wata Majami’ar Katolika ce ta shirya zanga-zangar a birnin Kinshasa a jiya Lahadi don nuna rashin amincewarta da yunkurin shugaba Kabila na ci gaba da kankamewa kujerar mulki duk da karewar wa’adinsa tun a cikin watan Disamban 2016.

Florence Marchal, ita ce mai magana da yawun rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a Jamhuriyar Demokradiyar Congo, ta kuma shaida wa RFI cewa, jami’an tsaronsu na bada gudun mawa don tabbatar da zaman lafiya da kuma dakile duk wani tashin hankali.

Marchal ta bukaci bangrorin biyu da su kaurace wa rikici saboda kauracewar na da matukar muhimmanci kamar yadda ta ce.

“Ya kamata a gudanar da duk wata zanga-zanga cikin lumana, sannan kuma jami'an tsaro su mayar da martinin da ya dace.” In ji Florence .

Rahoatnni na cewa, an raunata mutane 57 tare da kama gommai a sassan kasar saboda shiga zanga-zangar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.