Mahara sun bude wuta kan dakarun wanzar da zaman lafiya a Bangui
Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da kisan dakarunta da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya inda ta ce wasu yan bindiga ne suka bude wuta kan sansanin dakarun na ta da ke birnin Bangui na kasar.
Wallafawa ranar:
Sanarwar da Majalisar ta bayar, ta nuna cewar an kai harin ne da misalin karfe 11 na dare a gidajen da dakarun kasashen Masar da Jordan ke zama, abinda ya haifar da musayar wuta tsakanin dakarun da Maharan.
Vladimir Monteiro, mai magana da yawun Majalisar ya ce ya zuwa yanzu basu kai ga gano wadanda suka kai harin ko kuma wadanda ke da hannun a kitsa shi ba.
Haka zalika Majalisar ba ta fayyace adadin Dakarun da suka kwanta dama ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu