Isa ga babban shafi
Najeriya

Amurka za ta tallafawa Najeriya wajen yakar Boko Haram

Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson ya ce Kasarsa za ta ci gaba da tallafawa Najeriya ta fannonin da suka shafi yaki da ta'addanci dama ababen more rayuwa. Tillerson wanda ke sanar da hakan yayin ganawarsa da shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari a ziyarar da yake karkarewa yau a Nahiyar ta Afrika a shirye su ke su kara dankon alaka da Najeriyar.

Sakataren harkokin wajen Amurkar zai shafe sa’o’I kalilan ne a Najeriyar kafin daga bisani ya hau jirgi zuwa birnin Washington DC na Amurka.
Sakataren harkokin wajen Amurkar zai shafe sa’o’I kalilan ne a Najeriyar kafin daga bisani ya hau jirgi zuwa birnin Washington DC na Amurka. REUTERS/Mohamed Azakir/Files
Talla

Tillerson yayin ziyarar ta sa wadda ya sauka a Abuja babban birnin Najeriyar bayan tasowa kai tsaye daga filin jirgin saman N’Djamena na Chadi ya gana da jami’in Ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja kafin daga bisani kuma ya samu ganawa da shugaban Najeriyar dama sauran manyan jami’an gwamnatin kasar.

Sakataren harkokin wajen Amurkar zai shafe sa’o’I kalilan ne a Najeriyar kafin daga bisani ya hau jirgi zuwa birnin Washington DC na Amurka.

Ziyarar ta Tillerson dai na da nufin wanke katobarar da mai gidansa Donald Trump ya tafka kan Nahiyar ta Afrika inda ya kira shugabanninta da wawaye.

Kafin yanzu dai an tsara cewa Tillerson din zai isa Njaeriyar a gobe Talata, amma saboda dalilai na lafiyarsa ya sauya tsarin tafiyar don ya gaggauta komawa gida, ko da yake dai daga bisani babban jami’in da ke kula da lafiyarsa ya sanar da cewa ya samu cikakkiyar lafiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.