Isa ga babban shafi
Amurka

Tillerson ya kammala ziyarar sa ta farko a yankin Asia

Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson ya kammala ziyarar sa ta farko a yankin Asia, in da ya cim-ma yarjejeniyar yin aiki tare da China don sauya matsayin Koriya ta Arewa kan gwaje-gwajen makami mai linzami.

Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson
Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson REUTERS/Kevin Lamarque/File Photo
Talla

Kazalika bangarorin biyu sun kuma cim-ma matsaya don jingine sabanin da suke samu kan Taiwan da China ke kallo a matsayin yankinta.

China dai ta fusata bayan Amurka ta bukace ta da ta sanyo ido kan shirin mallakar makami mai linzami na Koriya ta Arewa da kuma matakin Amurkan na girke manyan na’urorin tinkarar makaman masu linzami a Koriya ta Kudu.

Kazalika China na zargin take-taken Amurkan kan Taiwan da China ke kallo a matsayin wani yankinta, yayin da gwamnatin Donald Trump ke shirin bai wa yankin makamai, matakin da ake ganin ya harzuka China.

Sai dai a ganawar da suka yi a birnin Beijing a karshen mako, shugaban China Xi Jinping da sakataren harkokin wajen na Amurka Rex Tillerson duk sun jingine sabanin da ke tsakanin kasashen biyu a gefe.

Shugaba Xi ya ce, Tillerson ya taka rawa sosai don maido da kyakkyawar danganta tsakanin kasashen biyu a karkashin gwamnatin Donald Trump.

Xi ya kara da cewa, ya gana da Trump ba adadi ta wayar tarho da kuma musayar sakwannin kar ta kwana.

Mista Tillrson ya ce, Amurka da China za su yi aiki tare don tabbatar da sauya shirin Koriya ta Arewa kan makamin Nukiliya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.