Isa ga babban shafi
Amurka-Rasha

Fadar Rasha za ta hana Tillerson ganawa da Putin

Fadar gwamnatin Rasha ta ce ba za ta bai wa Sakataren Harkokin Wajen Amurka Rex Tillerson damar ganawa da shugaba Vladimir Putin ba a  yayin ziyarar da zai kai kasar a gobe Laraba.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Rex Tillerson  da shugaban Rasha Vladimir Putin
Sakataren Harkokin Wajen Amurka Rex Tillerson da shugaban Rasha Vladimir Putin REUTERS/Alexsey Druginyn
Talla

Cikin wata sanarwar da ta fitar gabanin ziyarar, gwamnatin Rasha ta ce sai dai Tillerson ya gana da takwaransa, Ministan Harkokin Wajen kasar Sergei Lavrov.

Ko da ya ke har yanzu kakakin gwamnatin Rasha Dmitry Peskov bai bayyana dalilin soke ganawar Tillerson da shugaba Putin ba, yayin da ake hasashen cewa matakin zai  karfafa tsamin dangantaka tsakanin kasashen biyu.

A lokacin zantawa da manema labarai a Moscow, Ditry Peskov ya ce, babu wani shiri a kasa kan ganawar Tillerson da shugaba Putin, don haka tilas ya bi tsarin ganawa da takwaransa Sergei Lavrov.

Dama dai akwai jikakkiya tsakanin kasashen biyu musamman kan harin martanin da Amurka ta kai wa gwamnatin Syria a makon jiya bisa zargin ta da kai harin makami mai guba kan fararen hula a lardin Idlib da ke karkashin ikon ‘yan tawaye, zargin da Rasha ke ci gaba da musantawa tare da ikirarin za ta ci gaba da goyon bayan gwamnatin Bashar al-Assad.

Yanzu dai lokaci kawai zai nuna sakamakon da zai fito bayan wannan ziyara, kasancewar tun kafin harin martanin da Amurka ta kai kan Syria, akwai banbance- banbancen da ke bukatar zama a teburin shawara tsakanin kasashen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.