Martanin kasashen duniya kan harin Amurka a Syria
Kasashen Rasha da Iran sun yi Allah wadai da hare haren saman da Amurka ta kaddamar a cikin Syria wanda ya hallaka sojojin kasar guda 4.
Wallafawa ranar:
Kakakin fadar shugaban Rasha Dmitry Peskov, ya ce matakin da Amurka ta dauka zai kara tabarbarewar al’amura ganin irin matsalolin da suka adabi kasar
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Bahram Ghassemi ya ce suna adawa da duk wani shirin kai hari ko daukar matakin soja a Syria.
Ita kuwa Birtaniya tabi sahun Israila da Saudiya ne wajen goyan bayan harin.
Suma ‘yan tawayen Syria sun bukaci ci gaba da kai hare haren.
Kakakin ‘yan Tawayen, Ahmad Ramadan ya ce daukacin ‘yan adawar kasar na yabawa da wannan mataki, kuma suna bukatar ganin an fadada shi.
Tashar talabijin din Syria ta ruwaito cewar harin ya yi mummunar ta’adi, kuma suna daukar matakin a matsayin wani nuna karfi.
Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yaba da abinda ya kira babban sakon da aka aikewa shugaba Assad.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu