Isa ga babban shafi
Tunis

Zanga-zangar Tunisia ta dauki sabon salo

Jagoran zanga-zangar Tunisia da aka shafe kusan kwanaki goma ana gudanarwa, Warda Atig ya jaddada kudurinsu na ci gaba da aiwatar da zanga-zangar duk da kamen da ake ci gaba da yi. Fiye da mutane 800 ne yanzu haka ke rike a hannun Gwamnati tun bayan fara zanga-zangar a makon jiya don adawa da halin matsin da al’umma ke ciki.

Daruruwan jama'a ciki har da mata da kananan yara yayin wani gangamin murnar cika shekaru 10 da hambarar da gwamnayin Shugaba Zeinil Abidin bin Ali.
Daruruwan jama'a ciki har da mata da kananan yara yayin wani gangamin murnar cika shekaru 10 da hambarar da gwamnayin Shugaba Zeinil Abidin bin Ali. ©REUTERS/Youssef Boudlal
Talla

A cewar Warda Atig a yau kadai an kama fiye da mutane 40 inda ya ce za su ci gaba da gangamin har zuwa lokacin da bukatarsu za ta biya tare da sako tarin jama’ar da aka kama.

Bayan lafawar zanga-zangar a ranar Juma’ar da ta gabata a Lahadin makon jiya zanga-zangar ta dawo sabuwa tare da juyewa zuwa tarzoma bayan da al’umma suka amsa kiran kungiyoyin fafutuka lamarin da ya sa gwamnati kara daukar matakan kame bayan tun da farko ta bukaci a kwantar da hankula tare da alkawarta samar da sauye-sauye.

Ko a shekarar 2011 anyi makamanciyar zanga-zangar da ta kai ga kawar da gwamanti shugaba Zainul-Abidine Bin Ali, shugaban kasar Larabawa na farko da 'yan kasarsa suka tuge shi daga karagal mulki.

Wata kididdiga da majalisar dinkin duniya ta fitar ta nuna cewa mutane 200 daga cikin 800 da gwamnatin Tunisia ta kama sakamakon zanga-zangar dukkaninsu matasa ne da shekarunsu bai gaza 15 zuwa 20 ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.