Isa ga babban shafi
Najeriya

Birtaniya da Faransa sun musanta mara baya ga IPOB

Kasashen Faransa da Birtaniya sun musanta hannunsu a mara baya ga ayyukan kungiyar nan ta IPOB mai fafutukar kafa kasar Biafra, kungiyar da a baya-bayan nan hukumomin Najeriya suka ayyana ta a matsayin kungiyar ta’addanci.

Kasashen na Faransa da Birtaniya sun musanta ikirarin cewa suna bayar da gudunmawa ga kungiyar ta IPOB mai fafutukar kafa kasar Biafra a Najeriya.
Kasashen na Faransa da Birtaniya sun musanta ikirarin cewa suna bayar da gudunmawa ga kungiyar ta IPOB mai fafutukar kafa kasar Biafra a Najeriya. REUTERS
Talla

Kasashen biyu sun yi ikirarin cewa gwamnatin Najeriya ba ta tuntubesu ba, kafin sanar da sunayensu a matsayin masu mara baya ga ayykan kungiyar ta IPOB.

Ofishin Jakadancin Faransa a Najeriyar cikin wata sanarwa da ya fitar, Jakanda Mr Claude Abily ya ce ya girgiza matuka da kalaman ministan yada labaran na Najeriya Alhaji Lai Muhammad wanda ya bayyana Faransa a matsayin mai mara baya ga ayyukan kungiyar.

Mr Abily ya ce ba su da wata masaniya kan harkokin kungiyar a Faransa ita kuma gwamnatin Najeriya ba ta tuntubesu kafin fitar da sanarwar ba.

Sanarwar ta ce a shirye Faransa ta ke ta bayar da dukkanin wasu bayanan tsaro da ta ke da su kasancewar tana goyon bayan ci gaba da zaman Najeriya a matsayin kasa daya dunkulalliya.

Itama dai Birtaniya ta musanta ikirarin da gwamnatin Najeriyar ta yi na cewa ta ki amincewa da Rufe Radio Biafra, inda Sanarwar da Ofishin jakadancin Birtaniyar ya fitar dauke da sa hannun jami’in yada labarai Loe Abuku ta ce Najeriya bata aikewa Birtaniya da bukatar rufe Radiyon ta Biafra ba.

A jiya Alhamis ne dai ministan yada labaran Najeriya Alhaji Lai Muhammad ya sanar da cewa sun gano shalkwatar da kudade ke zuwarwa kungiyar ta IPOB a Faransa, yayin da kuma ya ce Birtaniya ta ki amincewa da bukatar gwamnatin Najeriya kan rufe Radiyon Biafra da ke kasar, wadda ta nan ne kungiyar ke yada manufofinta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.