Kotun Najeriya ta ayyana IPOB a matsayin ta 'yan ta'adda
Babbar kotun tarayya da ke birnin Abuja ta bada umarnin ayyana kungiyar masu fafatukar kafa kasar Biafra, IPOB a matsayin ta ‘yan ta’adda
Wallafawa ranar:
Kotun ta bada umarnin ne bayan ministan shari’a kuma lauyan gwamnati, Abubakar Malami ya shigar da batun a gabanta a madadin gwamnatin tarayya.
Kotun ta kuma haramta ayyuakn kungiyar a dukkanin fadin Najeriya musamman a yankunan kudu maso gabashi da kudu maso kudu, in da masu fafutukar suka fi tayar da kayar baya.
Gabanin wannan matakin na kotun, rundunar sojin kasar ta ayyana kungiyar IPOB a matsayin ta ‘yan ta’adda, amma ta sha suka daga wasu bangarori da ke cewa, rundunar ba ta bi ka’ida ba kafin ayyana kungiyar a matsayin ta ‘yan ta’adda.
A bangare guda, gwamnatin Najeriya ta zargi cewa, masu fafutukar kafa Biafra na samun tallafin kudade daga kasashen waje.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu