Isa ga babban shafi
Africa ta Kudu-Zimbabwe

Grace Mugabe tana wasan buya da jami'an tsaro

Uwargidan shugaban kasar Zimbabwe, Grace Mugabe, taki halartar taron matan shugabannin kasashen yankin kudancin Africa, wanda aka fara shi a ranar Asabar, a Africa ta Kudu, da ya kamata a ce ta halarta.

Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe tare da uwargidansa Grace Mugabe yayinda suke halartartaron jam'iyyarsu ta ZANU (PF) a Chinhoyi, da ke Zimbabwe, ranar 29 ga watan Yuli da ya gabata.
Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe tare da uwargidansa Grace Mugabe yayinda suke halartartaron jam'iyyarsu ta ZANU (PF) a Chinhoyi, da ke Zimbabwe, ranar 29 ga watan Yuli da ya gabata. REUTERS/Philimon Bulawayo
Talla

Grace Mugabe dai tana cigaba da ikirarin Africa ta Kudu ta bata mafakar siyasa, bayanda da aka zarge ta da cin zarafin wata Mata a makon da ya gabata, ta hanyar gabza mata duka a kai, wanda hakan ya sabba wa matar samun rauni a kai.

Hukumomin Africa ta Kudu dai sun ce har yanzu tana kasar, kuma suna cigaba da nazari kan bukatar Grace Mugaben na neman su bata mafaka.

Tun a makon da ya gabata ne dai ‘yan adawar Zimbabwe, ke kiraye kirayen hukumomin tsaron Africa ta Kudu, su damke uwargidan shugaban nasu domin ta fuskanci hukunci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.