Isa ga babban shafi
Libya

'Yan tawayen Libya na garkuwa da bakin-haure

Hukumar kula da bakin haure a duniya ta bayyana takaicinta a game da wani hodon bidiyo da ke nuna yadda ‘yan tawayen Libya ke yin garkuwa da bakin haure domin samun kudaden fansa.

bakin haure a Libya
bakin haure a Libya AFP
Talla

Hoton bidiyon ya nuna wasu ‘yan ci rani daga kasashen Somalia da kuma Habasha su 260 a hannun wasu ‘yan tawaye da ke yankin kudancin Libya, kuma bidiyon ya nuna wasu daga cikinsu a zaune yayin da wasu ke kwance dukkaninsu a kasa, kuma ga alama sun tagayyara sakamakon yunwa.

A cikin bidiyon wanda wani dan jaridar kasar Turkiyya ya yada, daya daga cikin matasan da aka yi garkuwa da su yana kwance ne a kasa da kuma katon dutse an dora ma sa a baya.

An ji wannan matashi na cewa, an yi masa haka ne saboda ya gaza biyan dala dubu 8 a matsayin kudin fansa, inda ya ce an yi masa duka har ma an karya ma sa hannnu tare da cire ma sa haure, kafin daga bisani a dora masa dutse a doron bayansa.

Hukumar kula da bakin haure ta duniya ta ce wannan abin assha ne, lura da cewa ana tsare da mutanen ne a wani yanki da ba kungiyoyin agaji balanta wadanda za su shiga tsakani domin ceto mutanen da ake garkuwa da su.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.