Isa ga babban shafi
Chadi

Takaddama ta kaure a shirin taron kasa a Chadi

Jam’iyyun adawa a kasar Chadi sun nuna rashin amincewarsu dangane da irin mutanen da gwamnatin kasar ke neman gayyata domin halartar wani taro da nufin yi wa dokokin kasar gyara.

'Yan adawa sun soki gwamnatin Deby kan mamaye taron kasa
'Yan adawa sun soki gwamnatin Deby kan mamaye taron kasa REUTERS/Moumine Ngarmbassa
Talla

Wasu daga cikin gyare-gyaren da ake son taron ya amince da su har da kayyade wa’adin shugabancin kasar domin ya kasance sau biyu kacal.

Amma ‘yan adawar na ganin cewa mutanen da ake neman gayyata domin tattauna wannan batu ba su wadatar ba.

Jagoran ‘yan adawar Saleh Kebzabo na ganin cewa duk wani batu da ya shafi yi wa dokokin kasar gyara ya kamta a ba su damar bayyana matsayinsu.

A cewarsa, Jam’iyyun siyasa akalla 60 ake da su a Chadi kuma sun yi imani da cewa kasar na cikin matsala, saboda haka akwai bukatar bayar da dama ga kowa don tofa albarkacin bakinsa ba wai a tara wani gungu na mutane kalilan domin shata wa kasar makoma ba, abin da ake bukata shi ne a wadanda za su iya gabatar da hujjojin da suka dace.

Sai dai mai Magana da yawun jami’iyyar da ke kan karagar mulkin kasar Jean Bernard Batre, ya ce yi wa hukumomin wannan kasa gyara na daga cikin alkawullan yakin neman zaben da suka bai wa shugaban kasa nasara kuma babbar fatansu shi ne aiwatar da gyare-gyaren da za su karfafa hukumomi da ma’aikatun gwamnatin Chadi.

Mista Batre ya ce batun kiran babban taro tare da gayyato kowa da kowa ciki har da jam’iyyun siyasa domin ba su damar tsoma bakunansu, wannan tamkar kauce wa manufa ne.

Yanzu haka dai Shugaba Idris Deby na kan wa’adin shugabancin kasar ta Chadi ne karo na biyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.