Tarayyar Afrika ta goyi bayan yarjejeniyar Paris ta canjin yanayi
Kungiyar Tarayyar Afirka AU ta bayyana cikakken goyan bayanta ga yarjejeniyar magance matsalar sauyin yanayin da aka kulla a Paris, tare da yin allawadai da matsayin shugaba Donald Trump na yin watsi da yarjejeniyar.
Wallafawa ranar:
Kungiyar AU ta ce gurbata yanayin da masana’ntun manyan kasashe ke yi, ya fi yi wa nahiyar illa a duniya.
Shugaban Guinea kuma shugaban kungiyar Alpha Conde ya bukaci a tattauna batun canjin yanayin a taron kasashe 20 masu karfin tattalin arziki na G20 da za a gudanar a Jamus a watan gobe.
Shugaba Conde ya ce akwai bukatar a wayar wa Trump kai kan illolin dumamar yanayi a duniya.
A ranar Alhamis ne shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da yin watsi da yarjejeniyar ta Paris da aka amince a 2015.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu