Isa ga babban shafi
G7

G7 sun bukaci sa ido a shafukan ‘Yan ta’adda a Intanet

Shugabannin kasashe bakwai masu karfi tattalin arzikin duniya da ake kira G7 sun bukaci kamfanonin sadarwa a Intanet su inganta daukar matakan yakar ayyukan masu tsattsauran ra’ayi a kafofin sadarwa.

Shugabannin kasashen G7 a Sicily yankin Italiya
Shugabannin kasashen G7 a Sicily yankin Italiya REUTERS/Jonathan Ernst
Talla

Shugabannin sun amince su karfafa daukar matakan yaki da ta’addanci musamman bayan mummunan harin da aka kai a Manchester a Birtaniya.

Taron na G7 ya kuma tattauna batututwa da suka shafi kasuwanci da canjin yanayi batutuwan da suke da sabani akai tsakaninsu da sabon shugaban Amurka Donald Trump wanda ya halarci taron a karon farko da ake gudanarwa a Sicily na Italiya.

Tuni dai shugaban kungiyar Tarayyar Turai Donald Tusk ya danganta taron a matsayin a mafi kalubale musamman ga manofofin da ake son cim ma.

Yarjejeniyar Canjin yanayi
Firaministan Italiya da ke jagorantar taron ya ce babu wani ci gaba da aka samu kan sabanin da ke tsakanin kasashen Turai da Amurka kan canjin yanayi.

Kasashen G7 sun kunshi Faransa da Birtaniya da Jamus da Canada da Amurka da Japan da Italiya da shugabanninsu ke tattaunawa da taron tare da wakilan Tarayyar Turai.

Taron shi ne na farko ga Emmanuel Macron, na Faransa da Theresa May Firaministan Birtaniya da kuma takwaranta na Italiya Paolo Gentiloni.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bukaci takwaransa na Amurka Donald Trump ya tsaya ya yi nazari sosai kafin yanke hukuncin akan yarjejeniyar canji yanayi ta Paris.

Trump ya ce idan ya kammala ziyararsa ta farko a kasashen duniya zai sanar da matsayinsa akan yarjejeniyar da kasashe 196 suka sanyawa hannu a 2015 a birnin Paris

Shugaba Macron ya ce baya son Amurka ta yi gaggawar yanke hukunci akan yarjejeniyar canjin yanayin ta Paris.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.