Isa ga babban shafi
Amurka

Trump ya yi watsi da yarjejeniyar Paris ta canjin yanayi

Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da yin watsi da yarjejeniyar canjin yanayi da kasashe 197 suka amince a Paris a bara domin rage dumamar yanayi a duniya. Amma ya ce zai yi kokarin samar da wata yarjejeniyar ta canjin yanayi.

Shugaban Amurka Donald Trump ya cika alkawalin watsi da yarjejeniyar Paris ta canjin yanayi
Shugaban Amurka Donald Trump ya cika alkawalin watsi da yarjejeniyar Paris ta canjin yanayi REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

Trump ya ce daga yau ya warware yarjejeniyar Paris bisa tsaurinta da nauyinta da ke barazana ga tattalin arzikin Amurka.

A cikin jawabinsa Trump ya ce yarjejeniyar ta yi sassauci ga China da India, daya daga cikin kasashen duniya masu manyan masana’antu da ke gurbata muhalli.

Nan take ne dai Tsohon Shugaban Amurka Barack Obama da ya amince da yarjeniyar ya mayar da martani ga Trump yana mai cewa shugaban ya yi watsi da makoma mai kyau ga duniya.

Yarjejeniyar Paris dai ta kunshi rage gurbataccen iska da ke gurbata muhalli sakamakon ayyukan masana’antun manyan kasashe da ke haifar da matsalolin dumamar yanayi tare da biyan kudade ga kananan kasashe da matsalar ta fi yi wa illa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.