Isa ga babban shafi
Paris

Paris: An cim ma matsaya kan rage dumamar yanayi

Kasar Faransa da ke jagorantar taron magance matsalar sauyin yanayi a Paris tace an cim ma yarjejeniya tsakanin wakilan kasashe 195 a yau Assabar bayan shafe kusan mako biyu ana muhawara kan batun.

An shafe makwanni biyu wakilan kasashe 195 na tattaunawa kan yarjejeniyar sauyin yanayi
An shafe makwanni biyu wakilan kasashe 195 na tattaunawa kan yarjejeniyar sauyin yanayi REUTERS/Jacky Naegelen
Talla

Ofishin Ministan harakokin wajen Faransa Laurent Fabius ya ce idan an jima ne da misalin karfe 10:30 agogon GMT za a gabatar da daftarin yarjejeniyar ga ministocin kasashen duniya a taron.

Sai dai zuwa yanzu babu wani cikakken bayani akan abinda ke cikin daftarin yarjejeniyar da wakilan ministocin muhalli na kasashen duniya za su sanyawa hannu.

Ana son dai rage gurbataccen iska ne da ke gurbata muhalli sakamakon ayyukan masana’antun manyan kasashe da ke haifar da matsalolin dumamar yanayi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.