Isa ga babban shafi
Nijar

'Yan adawa ba su amince da rahoton binciken kudin Uranium ba

‘Yan adawa a Jamhuriyar Nijar sun yi watsi da sakamakon binciken da majalisar dokokin kasar ke shirin gabatar wa dangane da zargin da ake yi wa gwamnati na handame kudaden kasar da yawansu ya kai CFA bilyan 200 wadanda aka sama daga cinikin Uranium

France Siege d'Areva
France Siege d'Areva
Talla

Daya daga cikin wakilan ‘yan adawa a kwamitin da ya gudanar da wannan bincike, Honnorable Sumana Sanda, ya nisanta kansu da wannan da ake shirin gabatarwa, inda ya yi zargin cewa kwatimin ya ki karbar hujjojin da suka gabatar.

Ana zargin tsohon shugaban ma’aikata a fadar shugaban kasar wanda a halin yanzu yake rike da mukamin ministan kudi Hassoumi Massaoudou ne da hannu wajen handame kudaden.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.