Isa ga babban shafi
Najeriya

An cafke wasu mata da ke shirin kai hari a Borno

Jami’an tsaron Civil Defence reshen jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya sun sanar da cafke wasu mata biyu da ake zargin cewa suna shirin kai hare-hare ne a yankin

Mata yan Boko Haram yanzu ke kai haren haren kunar bakin wake a Najeriya
Mata yan Boko Haram yanzu ke kai haren haren kunar bakin wake a Najeriya STRINGER / AFP
Talla

Jami’an tsaron sun bayyana daya daga cikinsu da cewa matar Mamman Nur ce wato shugaban kungiyar Boko Haram da ya balle, kuma an bayyana sunayen matan a matsayin Amina Shu’aibu da Fatima Muhammad Kabir wadanda aka kama a tashar motar Maiduguri.

Wasu rahotanni sun ce ‘Yan Boko Haram bangaren Abu Musab Barnawi sun kashe Sojoji 5 tare da raunana wasu bayan sun bude wuta a wani shingen binciken jami’an tsaro a Maiduguri.

Yanzu dai hare hare kan jami’an tsaro sun fara yawaita a Borno inda yanzu sau biyu ke nan ana kai hari shingen bincikensu a cikin mako guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.