Isa ga babban shafi
Najeriya

Sojojin Najeriya sun kashe 'yan Boko Haram 21

Rundunar Sojin Najeriya ta sanar da hallaka mayakan kungiyar Boko Haram 21 a kauyen Jarawa da ke karamar hukumar Kale Balge a Jihar Barno.

Sojojin Najeriya da ke yaki da Boko Haram a jihar Borno da ke yankin arewa maso gabashin kasar.
Sojojin Najeriya da ke yaki da Boko Haram a jihar Borno da ke yankin arewa maso gabashin kasar. AFP PHOTO/SUNDAY AGHAEZE
Talla

A cikin wata sanarwa da ta fitar, rundunar ta ce ta kuma ceto mutane dubu 1 da 623 da mayakan Boko Haram suka yi garkuwa da su.

Daraktan yada labaran rundunar, Janar Sani Usman Kuka sheka ya ce, yanzu haka an kai wadannan mutane da aka ceto zuwa wani sansanin ‘yan gudun hijira da ke Rann, yayin da aka yi wa yaran da ke cikinsu rigakafin kamuwa da cutuka.

Janar Usman ya kara da cewa sojojin na Najeriya sun kakkabe ‘yan ta’addan Boko Haram daga garuruwan Deima da Artano da Saduguma da Duve da Bardo da Kala da Bok da Msherde da kuma Ahirde.

Sojojin sun kuma kwace makaman Boko Haram da suka hada da manyan bindigogi samfurin AK-47 da kananan bama-bamai da addina da kuma babura.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.