Isa ga babban shafi
Amurka

Buhari ya tattauna da Trump ta tarho

Shugaban Amurka Donald Trump ya tattauna da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ta wayar Tarho a yau da misalin karfe 3:45 na yamma agogon Najeriya. Buhari ya tattauna da Trump ne daga muhallinsa da ya ke hutu a London.

Shugaban Amurka Donald Trump zai tattauna da Buhari na Najeriya ta wayar Tarho
Shugaban Amurka Donald Trump zai tattauna da Buhari na Najeriya ta wayar Tarho REUTERS/Jonathan Ernst
Talla

A cikin sanarwar da Femi Adeshina ya fitar kakakin shugaban Najeriya, ya bayyana cewa shugabannin biyu sun tattauna yadda za su inganta huldar tsaro domin yakar ta’addanci.

Trump ya yaba wa Buhari musamman kan kubutar da wasu daga cikin ‘yan matan Chibok tare alkawalin taimakawa Najeiya da makamai.

Sannan a tattaunawar, Buhari ya taya Trump Murnar nasarar zaben shugaban kasa, inda Trump kuma ya gayyace shi zuwa fadar White House.

Malam Garba Shehu mai magana da Yawun shugaban Najeriya ya shaidawa RFI Hausa cewa tattaunawar kuma  tsakanin shugabannin biyu ta mayar da hankali a game hulda da tsakanin Amurka da Najeriya.

Trump kuma ya zanta da shugaban Afrika ta kudu Jacob Zuma bayan ya tattauna da Buhari ta wayar tarho.

Wannan ne dai karon farko da Shugaban Amurka Donald Trump ya tattaunawa da shugabannin Afrika tun rantsar da shi a watan Janairu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.