Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya gana da shugabannin APC a London

Shugabannin Jam’iyyar APC da ke mulki a Najeriya sun ziyarci Shugaba Muhammadu Buhari a London inda ya ke gudanar da hutun rashin lafiya.

Nigerian President on medical leave with APC leaders in London 9 feb 2017
Nigerian President on medical leave with APC leaders in London 9 feb 2017 twitter
Talla

Shafin Twitter na Shugaban Najeriyar ya nuna Buhari zaune sanye da jallabiya a falo yana ganawa da tsohon gwamnan Lagos Bola Ahmed Tinubu jagoran APC da kuma shugaban Jam’iyyar Cif Bisi Akande da suka kai masa ziyara a London.

Buhari ya gana da Shugabannin APC a London

Hoton dai ya nuna Buhari da Tinubu suna murmushi a lokacin da suke tattaunawa.

Batun rashin lafiyar Buhari dai ya canjo cece-kuce bayan ya tsawaita wa’adin hutun da ya dauka na kwanaki 10 inda Wasu ‘Yan kasar ke ganin tsawaita hutun ya tabbatar da shugaban ba ya cikin koshin lafiya.

Sanarwar da fadar shugaban kasar ta fitar ta ce, likitansa ne ya bukaci ya tsawaita hutun domin samun damar kammala gwaje gwaje da kuma samun sakamako.

 Fadar shugaban ta nanata cewa shugaban na cikin koshin lafiya ba tare da bayyana ainihin rashin lafiyar da ya ke fama da ita ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.