Isa ga babban shafi
Najeriya

Majalisar Najeriya ta karbi wasikar Buhari

Majalisar Dattawan Najeriya ta tabbatar da karbar wasikar da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya aiko mata, in da ya sanar da tsawaita hutunsa a birnin London don duba lafiyarsa.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Talla

Sai dai Majalisar ba ta bada cikakken bayani ba game da abubuwan da wasikar shugaban ta kunsa.

A ranar Lahadin da ta gabata ne fadar shugaban kasar ta sanar cewa, an tsawaita hutun kwanaki 10 na Buahri bayan likitocinsa sun bukaci haka don yi masa wasu gwaje-gwaje.

Amma kawo yanzu, fadar shugaban kasar ba ta sanar da takamamman ranar da shugaba Buhari zai dawo Najeriya ba, yayin da ci gaba da zamansa a London ya  haifar da cece-kuce a Najeriya, in da wasu ke ganin cewa, ba a fayyace musu hakikanin halin da shugaban ke ciki ba.

Sai dai mukaddashin shugaban kasar, Farfesa Yemi Osinbajo ya tabbatar wa ‘yan kasar cewa, Buhari na cikin koshin lafiya kuma ana saran dawowarsa nan bada jimawa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.