Ana gudanar da babban zabe a Somalia
Al'ummar Somalia na gudanar da zaben shugaban kasa a yau Laraba, bayan jinkirin watanni da aka samu.
Wallafawa ranar:
Shugaba Hassan Sheikh Mahmud na neman wa'adi na biyu tare da wasu ‘yan takara 21 da ke kokarin raba shi da kujerasa.
Somalia dai ta fada cikin tashin hankali tun bayan kifar da gwamnatin shugaba Siad Barre a shekarar 1991, yayin da kuma take fama da hare-haren ta'addanci daga mayakan al shebab.
Shugaba Mahmud ya ce, jami'an 'yan sanda za su bada kariya a rumfuna zabe da kuma unguwanni a yayin gudanar da zaben.
Kazalika zaben na zuwa ne a dai dai lokacin da ake fargabar tsindimar kasar cikin matsalar karancin abinci sakamakon fari.
Dukkanin 'yan takaran sun yi alwashin samar da tsaro da kuma inganta tattalin arzikin Somalia.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu