Isa ga babban shafi
Amurka

Kasashen da dokar hana shiga Amurka ta shafa na cigaba da maida raddi

Kasashen da Amurka ta haramtawa ‘ya’yansu shigarta, na cigaba da maida raddi kan kudurin da shugaban kasar Donald Trump ya sakawa hannu.

Masu zanga zangar adawa a birnin London kan matakin shugaban Amurka Donald Trump na haramtawa Muslmi shiga kasar.
Masu zanga zangar adawa a birnin London kan matakin shugaban Amurka Donald Trump na haramtawa Muslmi shiga kasar. BEN STANSALL / AFP
Talla

Zuwa yanzu dai, tuni da dama daga cikin cikin kasashen da wannan doka ta shafa suka maida martani, yayinda har yanzu wasu basu ce komai ba.

A martaninsa game da dokar takaita shigar Muslmin da baki ‘yan gudun hijira Amurka, Mataimakin shugaban kasar Iran Eshaq Jahangiri wanda ya bayyana dokar a matsayin cin zarafi, cewa yayi Iran zata dauki makamancin matakin kan yan kasar Amurka da ke san shiga kasar.

Ita kuwa ma’aikatar harkokin waje ta kasar Yemen cewa ta yi ba zata lamunci duk wani yunkuri na daukar kasar ko ‘ya’yanta a matsayin tushen ta’addanci ba, tare da bukatar shugaban Amurka Donald Trump ya sake tunani.

A kasar Sudan kuma wadda ke fafutukar a cire ta daga jerin kasashen da ke taimakawa ta’addanci da Amurka ta wallafa, sammacin jakadan Amurka a kasar aka yi zuwa ma’aikatar harkokin wajen Sudan din don jin yadda aka haihu a ragaya.

A bangaren kasashen Libya, Syria da kuma Somalia kuwa, zuwa yanzu babu wani martani a hukumance da kasashen suka fitar, sai dai wani shahararren dan wasan motsa jiki, dan salain kasar Somalia, MO Farah ya soki matakin na Trump a shafinsa na facebook, tare da bayyana takaicin rashin tabbas game da komawa wajen iyalansa, da yanzu haka ke kasar ta Amurka, bayan kammala atasayen da yake a kasar Habasha.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.