Isa ga babban shafi
Burundi

Burundi ta soma yiwa Fursinoni afuwa

Gwamnatin Kasar Burundi ta fara sakin kashi daya bisa hudu na mutanen da aka daure a gidan yari sakamakon afuwar da shugaban kasar ya yi musu.

Shugaban kasar Burundi, Pierre Nkurunziza
Shugaban kasar Burundi, Pierre Nkurunziza REUTERS/Evrard Ngendakumana
Talla

Kungiyoyin kare hakkin fursinoni na kokawa cewar an dauki matakin ne dan rage cunkoso da kuma samu sararin dauke fursinonin siyasa.

Cikin wadanda aka saka harda mutane 300 da ke gidan yarin Mpimba daga cikin 2,500 da ake kokarin sakewa baki daya.

Ministan shari’ar kasar Aimee Laurentine Kanyana ya ce an saki wasu masu fafutuka 58 da aka tsare a shekarar 2014 saboda shiga zanga zanga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.