Isa ga babban shafi
Gambia

Mataimakiyar shugaban Gambia Njie-Saidy ta yi murabus

Mataimakiya ga Yahya Jammeh ta yi murabus ne a yau Laraba kafin a rantsar da Adama Barrow a matsayin shugaban kasa a gobe Alhamis duk da shugaban kasar ya ki amincewa ya sauka.

Mataimakiyar shugaban Gambia Isatou Dijie-Saidy
Mataimakiyar shugaban Gambia Isatou Dijie-Saidy youtube
Talla

Murabus din Mataimakiyar ya nuna Yahya Jammeh ya rasa samun goyon bayan gwamnatin shi bayan kawo karshen wa’adin mulkin shi.

Wannan na zuwa bayan ministan ilimi mai zurfi Aboubakar Senghore ya yi murabus. Dukkaninsu sun ce ba su iya ci gaba da aiki ba bayan cikar wa’adin gwamnatin Jammeh.

Rahotanni sun ce gwamnatin Senegal ta ba Yahya Jammeh daga nan zuwa 12 na dare ya sauka ko kuma a yi amfani da karfi a tumbuke shi.

Wasu Majiyoyi sun tabbatar da ganin sojojin Senegal a kan iyakar Gambia a yau Laraba a wani mataki na shirin yaki da Yahya Jammeh bayan ya ki amincewa ya mika mulki ga Adama Barrow wanda ya lashe zaben kasar.

Daruruwan mutanen Gambia ne suka fice kasar zuwa Senegal kamar yadda baki ‘yan kasashen waje da suka je yawon bude ido ke ficewa.

Kungiyar ECOWAS da ke matsin lamba ga Jammeh, ta ce za a rantsar da Barrow a wani yanki na Gambia ba lalle sai Banjul ba fadar gwamnatin kasar, matakin da ke nuna za a samu hedikwatar gwamnati biyu a kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.