Isa ga babban shafi
Gambia

Jammeh ya ayyana dokar ta baci a Gambia

Shugaban Gambia mai barin gado Yahya Jammeh ya ayyana dokar ta baci ta tsawon kwanaki 90 a kasar, a daidai lokacin da ya rage 'yan sa’oi wa’adin mulkinsa ya kare.

Jammeh initially conceded defeat in the polls during an address on state television.
Jammeh initially conceded defeat in the polls during an address on state television. Photo: GRTS via AFP
Talla

Wannan na zuwa ne a yayin da shugabannin kasashen yammacin Afrika suka gaza shawo kan Jammeh don ganin ya mika mulki ga abokin hamayyarsa Adama Barrow da ya lashe zaben shugabancin kasar da aka gudanar a cikin watan Disamban bara.

A ranar Alhamis mai zuwa ne ya kamata a rantsar da Barrow don maye gurbin Jammeh da ya ki amince wa da shan kayi bayan ya zargi jami’an hukumar zaben kasar da tafka kura-kurai a zaben.

Tuni dai Jammeh ya shigar da kara kotun koli amma ta dage zaman shari’ar har zuwa watan Mayu mai zuwa saboda karancin alkalai, yayin da Jammeh ya jaddada cewa, ba zai sauka ba har zuwa lokacin da kotun za ta yanke hukunci.

Tuni dai dubban mutanen Gambia suka tsere daga kasar, in da suka nemi mafaka a kasar Senagel mai makwabtaka da su, yayin da Najeriya ta aike da jirgin yakinta don ci gaba da matsin lamba ga shugaban wanda ya mulki kasar na tsawon shekaru 22.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.